Isa ga babban shafi

Al'ummar Burkina Faso sun yi gangamin nuna goyon baya ga kyaftin Traore

Dubunnan al’ummar Burkina Faso sun gudanar da wani gangamin nuna goyon baya ga shugaban kasar Kyftin Ibrahim Traore yau Asabar a birnin Ouagadougou dai dai lokacin da ya ke cika shekara guda da kwace mulkin kasar a juyin mulkin da ya jagoranta.

Shugaban mulkin Sojin Burkina Faso kyaftin Ibrahim Traoré.
Shugaban mulkin Sojin Burkina Faso kyaftin Ibrahim Traoré. REUTERS - VINCENT BADO
Talla

Traore wanda ya kwace mulki daga hannun Damiba wanda shi ma ya hambarar da gwamnatin Roch Marc Christian Kabore, tun bayan da ya fara jan ragamar kasar ya sha alwashin kyautata tsaro cikin watanni 2 zuwa 3 a kasar mai fama da hare-haren ‘yan ta’adda.

Masu zanga-zangar wadanda ke ta furta kalaman goyon baya da karfafa gwiwa ga jagoran mulkin Sojin, a zantawarsu da manema labarai, sun ce an samu gagarumin ci gaba a yakin da kasar ke yi da ‘yan ta’adda.

Aïcha Ouedraogo guda cikin masu zanga-zangar ta shaidawa manema labarai cewa akwai matukar sauyi a kasar tun bayan hawan Traore, ta yadda hare-hare suka ragu aka kuma samu raguwar mutanen da tashe-tashen hankula ke rabawa da muhallansu a bangare guda wasu da yankunansu basa zaunuwa yanzu sun koma gida a yanzu haka bayan an fatattaki ‘yan ta’addan da suka addabesu.

Tun bayan hawansa mulki Traore ya katse alaka tsakanin kasar ta yammacin Afrika da Faransa uwar goyonta yayinda ya karkata alakarsa zuwa kasashen Rasha da Venezuela da kuma Iran, yayinda kuma ya tilasta ficewar ilahirin dakarun Faransa da ke kasar.

Haka zalika Traore ya karfafa sashen tsaron kasar ta hanyar daukar tarin sojoji ciki har da ‘yan sa kai wadanda ke bayar da tsaro a yankunansu.

Maxime Zongo da ke cikin masu gangamin, ya ce ko shakka babu shekara guda da Traore ya yi a kan mulki lokaci ne mai cike da tarihi lura da yadda zaman lafiya ya fara dawowa a yankunan karkara wadanda a baya rashin tsaro ya hanasu sukuni.

Ange Geoffroy Kabore da ke cikin mayakan sa kai, ya bayyana cewa fafutukar da su ke yi a yanzu,  suna yin ta ne don ‘ya’ya da jikokin Burkina Faso da za su zo a nan gaba, don haka basa fargabar rasa rayukansu a fagen daaga wajen kare al’ummarsu.

A cewar Kabore, shugaba Traore da kansa ya ke zuwa fagen daaga don karfafa musu gwiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.