Isa ga babban shafi

Tsaro da zaman lafiyar Burkina Faso ne mafi muhimmanci fiye da zabe - Traore

Dai dai lokacin da ake cika shekara guda da juyin mulkin Sojin Burkina Faso da ya bai wa kyaftin Ibrahim Traore damar jan ragamar kasar mai fama da hare-haren ta’addancin kungiyoyin masu ikirarin jihadi, jagoran mulkin Sojin kasar ta yammacin Afrika ya ce tsaro da zaman lafiyar al’ummarsa ne mafi muhimmanci fiye da kiran zabe.

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore.
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore. © AFP
Talla

A jawabinsa na kai tsaye ta gidan talabijin, kyaftin Traore wanda ya yi alkawarin shirya zaben shugaban kasa cikin watan Yulin badi, ya ce a yanzu abu mafi muhimmanci a gareshi shi ne samar da cikakken tsaron da zai bai wa al’ummarsa zaman lafiya.

A cewar shugaban dole a samar da sauyi ga kundin tsarin mulkin Burkina Faso ta yadda mulkin zai rika wakiltar ilahirin al’ummar kasar maimakon dankwafe wani bangaren.

Jawabin Traore yayin halartarsa taron tsaron kasashen Afrika a Rasha.
Jawabin Traore yayin halartarsa taron tsaron kasashen Afrika a Rasha. AFP - ALEXEY DANICHEV

Cikin jawabin na Traore ya ce tabbas gudanar da zaben na da muhimmanci amma tsaro da zaman lafiyar kasar shi ne mafi muhimmanci kuma shi ne al’umma suka fi damuwa da shi.

Jawabin na Traore na zuwa ne bayan gwamnatin Sojin ta Burkina Faso a Alhamis din da ta gabata ta sanar da kame wasu manyan sojoji 4 da ke da alaka da yunkurin juyin mulki a kasar.

A Larabar da ta gabata ne Burkina ta sanar da yadda Sojojin daga sashen tattara bayanan sirri na kasar suka yi yunkurin kifar da gwamnatin kyaftin Ibrahim Traore.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.