Isa ga babban shafi

Kotu ta baiwa tsohon shugaban Saliyo damar zuwa Najeriya don neman kulawar likitoci

Wata babbar Kotu a Saliyo ta umarci mahukuntan kasar da su baiwa tsohon shugaba Ernest Bai Koroma damar zuwa Najeriya domin neman magani.

Shugaban kasar Saliyo, Ernest Koroma
Shugaban kasar Saliyo, Ernest Koroma REUTERS/Joe Penney
Talla

Koroma ta bakin lauyansa ya bukaci a bashi damar tsallakawa zuwa Najeriya domin neman magani, sakamakon yadda yanayin rashin lafiya ya yi kamari.

 

Tsohon shugaban na Saliyo na tsare a hannun jami’an tsaro sakamakon zargin sa da hannu a kitsa Juyin mulkin da bai yi nasara ba, sai dai daga baya an bashi belin zama a iya gidan sa kawai, ko kuma ya nemi izinin fita daga babban sufeton ‘yan sandan kasar.

 

A baya dai gwamnatin kasar ta shirya gurfanar da Mr Koroma a gaban kotu ranar 17 ga watan Janairu, kasancewar dukannin hujjojinsu sun kammala amma kuma shugaban ya jewa kotu da wannan bukata.

 

Wannan na zuwa ne bayan da aka rika yada labarin cewa shugaban ya amince ya nemi mafaka a Najeriya matukar gwamnatin kasar zata janye dukannin tuhume-tuhumen da ake yi masa.

 

Da yake bayani ministan yada labaran kasar Chernor Bah ya ce gwamnati zata yi biyayya ga umarnin kotu , sai dai duk da haka tuhume-tuhumen da ake yiwa Koroma suna nan daram.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.