Isa ga babban shafi

Sudan ta dakatar da hulda da kungiyar kasashen gabashin Afirka

Gwamnatin sojin Sudan ta dakatar da hulda da kungiyar kasashen Gabashin Afrika IGAD, bisa zarginta da keta ‘yancinta na kasancewa yantattar kasa, ta hanyar gayyatar jagoran sojin kai daukin gaggawa zuwa taronta. 

Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban sojin Sudan.
Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban sojin Sudan. © AFP PHOTO / HO/ SAUDI PRESS AGENCY
Talla

Watanni 9 bayan fara rikici tsakanin sojojin kasar da kuma sojojin RSF, sojojin Sunda na rasa iko a mafi yawan yankunan da ke karkashinsu, yayin da jagoran RSF Modamed Hamdan Daglo ya fara ziyartar wasu kasashen da ke nahiyar. 

A ci gaba da samun karbuwa da yake yi, kungiyar IGAD ta gayyaci Daglo taronta da zai gudana a ranar Alhamis a Uganda kuma tuni a amsa gayyatar. 

Wannan mataki dai ya sanya ma’aikatar kulada harkokin wajen Sudan da ke biyayya ga Abdel Fattah al-Burhan ta sanar da dakatar da duk wata alaka da ke tsakaninsu da kungiyar. 

A ranar Asabar da ta gabata, ma’aikatar ta zargi kungiyar da bai wa Daglo dama, ciki harda halartar taronta da shugabannin kasashen da ke cikinta zasu halarta. 

Daglo ya fara rangadin wasu kasashen Afirka shida ciki har da mambobin kungiyar IGAD, yayin da manazarta ke ganin cewa babban hafsan sojan kasar na kara zama saniyar ware a sha’anin diflomasiyya, a dai-dai lokacin da dakarunsa ke ci gaba da wasun koma baya a hannun na RSF. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.