Isa ga babban shafi

Masu bada agaji na taro a Geneva kan taimakawa Sudan

A wannan litinin masu ba da taimako na kasa da kasa ke ganawa a birnin Geneva, domin agazawa wadanda rikicin Sudan ya shafa, ada-dai lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta na sa'o'i 72 tsakanin hafsoshin sojojin kasar biyu ke ba da damar kai kayan agaji ga mabukata.

Wasu 'yan gudun hijirar Sudan a Chadi.
Wasu 'yan gudun hijirar Sudan a Chadi. REUTERS - MAHAMAT RAMADANE
Talla

Bangarorin biyu sun sha amincewa da tsagaita wuta kan rikicin da ya lakume rayukan mutane sama da 2,000 tare da korar wasu miliyan biyu daga gidajensu, ciki har da kimanin 528,000 da suka yi gudun hijira a kasashen waje, amma ko so tari suna watsi tare da ci gaba da kai wa juna hare-hare.

A halin da ake ciki, Majalisar Dinkin Duniya na shirin gudanar da taron kasa da kasa da hadin gwiwar wasu kawayenta domin ganin yadda za’a taimakawa wadanda rikikicin Sudan ya shafa.

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, na cikin wadanda zasu gabatar da jawabi a taron da za a yi a yammacin wannan litinin a Geneva na kasar Swisland.

A cikin wata sanarwa da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ta yi fatan masu ba da agaji za su sanar ko alkawun tallafin kudi don magance matsalar jin kai a kasar, tare da jaddada bukatar bangarorin da ke rikici da juna a Sudan su mutunta hakkinsu a karkashin dokar agaji ta kasa da kasa.

Ya zuwa yanzu, asusun agajin jin kai ga Sudan ya samu kasa da kashi 16 cikin 100 cikin dalar Amurka biliyan 2.57 da ake bukata, yayin da shirin ba da agajin 'yan gudun hijira na yankin dake bukatan dala miliyan 470 ya samu kashi 17 cikin 100 kachal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.