Isa ga babban shafi

IOM tace akalla baki 61 suka nitse a tekun Medetereniya dake kusa da Libya

Afirka – Hukumar majalisar dinkin duniya dake sanya ido a kan kaurar baki ta IOM tace baki 61, cikinsu harda mata da yara kanana suka nitse a tekun Libya lokacin da kwale kwalen da suke ciki ya kife.

yadda baki ke wannan tafiya mai hadari a cikin teku
yadda baki ke wannan tafiya mai hadari a cikin teku AFP/File
Talla

IOM ta jiyo ta bakin wasu daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya a hatsarin na cewa, kwale kwalen su da ya tashi daga birnin Zwara dake da nisan kilomita 110 daga Tripoli, na dauke ne mutane 86.

Wasu daga cikin bakin da suka mutu a shekarar 2020 kusa da gabar ruwan Djibouti
Wasu daga cikin bakin da suka mutu a shekarar 2020 kusa da gabar ruwan Djibouti IOM, the UN Migration Agency

Hukumar ta bayyana cewar har ya zuwa wannan lokaci tekun Medetereniya na ci gaba da zama mafi hadari ga baki, abinda ke kaiga rasa rayukansu.

Daga cikin irin haduran da aka gani mafiya muni a wannan shekarar akwai hadarin da aka yi a watan Yuni, lokacin da wani jirgin kamun kifi mai dauke da mutane 518 ya nitse bayan ya bar Tobruk dake Libya zuwa Girka, inda ya hallaka mutane 78.

IOM tace a wannan shekarar ta 2023 baki sama da 2,200 suka mutu sakamakon irin wannan hadarin a teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.