Isa ga babban shafi

Sojojin dake mulkin Burkina Faso sun tilastawa wani fitacen dan farar hula shiga aikin soji

A kasar Burkina Faso, shugaban gungun kungiyoyin farar hular nan  da ke fada da rashin hukumta masu laifi, da kuma nuna tsangoma ga alúmma Daouda Diallo,  ya sake bayyana wani hoto da aka sha yadawa a shafukan sadarwar alúmma a jiya, sanye da hular soji. Bayan da ya yi batan dabo a ranar jumaár da ta gabata.

likita dan gwagwarmayar kare hakkin dan adama a Burkina Faso  Daouda Diallo, a watan Fabwaren  2022.
likita dan gwagwarmayar kare hakkin dan adama a Burkina Faso Daouda Diallo, a watan Fabwaren 2022. AP - Sophie Garcia
Talla

Tuni dai makusantansa suka tabbatar da cewa, suturar dake ga jikinsa  a ranar jumaár da aka yi awan gaba da shi ce ga jikinsa  a hoton da yake sanye da hular soji.

Tun dai kungiyoyin kare hakkin dan adam a kasar ta Burkina Faso suka yi zargin cewa, mahukumtan mulkin sojin kasar ne su ka sace shi, kamar yadda ake zargin gwamnatin Sojin da tilastawa masu sukarta shiga aikin soji karkashin wata dokar da ta  bukaci yin hakan idan kasa  ta na cikin rudu.

Matakin da kungiyoyin kare hakkin dan adam na ciki da wajen kasar suka yi tir da Allah waddai da shi

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.