Isa ga babban shafi

Kusan mutane 50 ne suka mutu a zabtarewar kasar da aka samu a Tanzania

Akalla mutane 47 suka mutu sannan wasu 85 suka jikkata a wani ifti’in zabtarewar kasar da aka samu sanadiyar ambaliyar ruwa a Arewacin Tanzania.

Yadda aka samu ambaliyar ruwa a garin Katesh a kasar Tanzania.
Yadda aka samu ambaliyar ruwa a garin Katesh a kasar Tanzania. AP
Talla

Kwamishinar da ke kula da yankin Janeth Mayanja, ta ce a ranar asabar da ta gabata ne dai, aka samu mamakon ruwan sama a garin Katesh da ke da nisan kilomita dari 3 daga babban birnin yankin Arewacin kasar, lamarin da ya haddasa iftila’in da ake ganin adadin wadanda suka mutu ya karu.

“Har zuwa wannan yammaci adadin wadanda suka mutu na nan a 47 sannan mutane 85 suka samu raunuka,” kamar yadda kwamishinar yankin Manyara da ke Arewacin Tanzania, Queen Sendiga ta bayyanawa manema labarai.

Shugabar Tanzania Samia Hassan da ke halartar taron Majalisar Dinkin Duniya COP28 a Dubai, ta jajantawa iyalan wadanda iftila’in ya shafa, tare da tabbatar da kokarin gwamnati wajen ceto wadanda suke makale.

Bayan fuskantar fari na tsawon lokaci da yankin Gabashin Afrika yayi, an kuma kwashe tsawon makwanni an maka ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya haddasa ambaliyar ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.