Isa ga babban shafi

Somalia ta shiga kungiyar kasashen gabashin Afirka

Somalia ta zama kasa ta 9 da ta shiga kungiyar hadin kan kasashen Gabashin Afrika, matakin da aka bayyana a matsayin babban ci gaba ga kasar da ke yankin kuryar gabashin Afrika, mai fama da rikicin ta’addanci.

Shugaban Somalia, Hassan Cheikh Mohammed.
Shugaban Somalia, Hassan Cheikh Mohammed. © HASSAN ALI ELMI / AFP
Talla

Somalia, mai yawan al’umma miliyan 17 ta shiga wannan kungiya ce a  daidai lokacin da take neman habaka kasuwancin bai- daya a fadin nahiyar.

A taron kungiyar da ta gudana a birnin Arusha na Tanzania ne aka sanar da karbar Somalia a kungiyar, inda yanzu ta hade da kasashe irin su Burundi, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Kenya, Rwanda, Sudan ta Kudu, Tanzania da Uganda.

Masu sharhi sun ce a yayin da wannan mataki ka iya zama ci gaba ta fannin tattalin arziki ga Somalia da makwaftanta, hakan na kuma iya haddasa wa kasashen kalubale na tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.