Rajoelina ya lashe zaben shugaban Madagascar a zagayen farko
An sake zaben Andry Rajoelina mai shekaru 49 a matsayin shugaban kasar Madagascar bayan zagayen farko na zaben da 'yan adawa goma suka kauracewa. A yau Asabar ne hukumar zaben kasar da aka sani da CENI ta fitar da wannan sakamako.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar kuma dan takara da yan adawa ke zarginsa da shirya magudi,Andry Rajoelina ya samu kashi 58.95% na kuri'un da aka kada a zagayen farko na zaben da aka gudanar a ranar 16 ga watan Nuwamba, bisa ga sakamakon da hukumar ta gabatar a wani taron manema labarai a Antananarivo.
Tun a ranar zaben ne,shugaban kasar mai ci Andry Rajoelina ya tabbatar da nasararsa a zaben da aka gudanar,zaben da yan adawa suka kaurace wa, inda sama da kashi uku na cibiyoyin kada kuri’a suka bayar da sakamakon.
Rajoelina, dan kasuwa kuma tsohon mai gabatar da mawaka DJ, wanda ya fara shugabantar kasar tsibirin tekun Indiya bayan juyin mulkin shekarar 2009.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu