Isa ga babban shafi
Zaben Madagascar

An bukaci dage gudanar da zaben shugabancin kasar Madagascar da karin mako guda

À Madagascar, shugabar majalisar dokokinkasar ta bukaci dakatar da gudanar da shirye shiryen zaben shugabancin kasar da akalla kwanaki  7 nan gaba. Ita dai wanan sanarwa ta hadin guiwa,  ta fito ne daga  kungiyar  addinin Kirstan kasar FFKM, sakamakon shiga tsakanin tattaunawar da aka kwashe tsawon kwanaki ana yi, da kuma ta biyo bayan  mako guda da aka kwashe  na tada jijiyoyin wuya, da kuma  zanga-zangar yan adawa.

Christine Razanamahasoa, shugabar majalisar dokokin kasar Madagascar
Christine Razanamahasoa, shugabar majalisar dokokin kasar Madagascar RFI/Marie Audran
Talla

A cikin wata sanarwar manema labarai a marecen jiya alhamis,  Christine Razanamahasoa, shugabar majalisar dokokin  ta bukaci ganin an dakatar da shirye shiryen gudanar da zaben  shugabancin kasar na ranar 16 ga nowambar nan da muke ciki 2023 tare da dakatar da yakin neman zabe da kuma dukkanin wasu tarurukan jama’a.

Manufar daga gudanar da zaben dai na faruwa ne domin baiwa tattaunawa damar samar da masalahar da zata samu amincewar kowa.

Ita dai wannan sanarwa neman daga gudanar da zaben shugabancin kasar ta Madagascar, a safiyar yau juma’a ta  samu saka hannun amincewar kimanin kungiyoyin farar hula da gwadago kusan 60

Sanarwar da tsohuwar maikawancen siyasa da shugaban kasar Andry Rajoelina, mai barin gado haka kuma dan takarar da ke neman maye kansa, ya kamata ta ko wane fanni ta farantawa hadin guiwar yan takara10, da a kulum ke nuna rashin amincewarsu dashiga yakin neman zaben, da suka ce, babu wasu kwararan matakai da aka dauka,  da za su tabbatar da an gudanar da zaben na demkradiya cikin haske da walwala

Daukar wannan matsayi dai, ya sake buda wani sabon babi, na hudar dake tsakanin jam’iya mafi rinjaye a kasar cewa da IRD.

A watan desemba da ya gabata, batun kuri’ar yankan kauna kan gwamnatin kasar da Ntsay ke jagoranta tuni ta haifar da baraka tsakanin shugaban kasar da kuma shugabar majalisar dokokin.

A gabe assabar ne da misalin karfe 9 na safiya a majalisar dokokin kasar ake sa ran shugabar majalisar dokokin za ta ganan da daukacin masu ruwa da tsaki dangane da shirya zabe a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.