Isa ga babban shafi

Rayuwar Dakarun Majalisa Dinkin Duniya na cikin hadari a Mali

Dakarun  wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun yi janyewar gaggawa daga sansanin su na Tessalit dake arewacin Mali kasancewar barazana da suke fuskanta ga rayuwarsu.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na MINUSMA a yayin atisaye a Mali
Dakarun wanzar da zaman lafiya na MINUSMA a yayin atisaye a Mali AFP - SIA KAMBOU
Talla

A ranar asabar 21 ga watan Oktoban 2023 ne   dakarun sojin Mali suka karbi ikon sansanin na Tessalit bayan da dakarun wanzar da zaman lafiya na MINUSMA suka janye a karo na farko a yankin Kidal dake fama da tashin tashina.

Sai dai ficewar dakarun na MINUSMA daga wannan yanki bayan shafe sama da shekaru 13 suna aikin wanzar da zaman lafiya na sanya fargabar yiwuwar barkewar sabon rikici a tsakanin dakarun kasar da na ‘yan tawaye masu rike da makamai a fafutukar neman mallakar ikon yankin.

Dakarun sun kammala janyewa a cikin mawuyacin hali mai cike da kalubale na tsaro wanda ya sanya jami’an samun kansu cikin hadari. Inji MINUSMA

Kafin janyewar dakarun wanzar da zaman lafiyar na Majalisar dinkin duniyar a yankin sun dauki tsauraran matakai na lalata kayakin da ba zasu iya tafiya dasu ba wanda suka hada da motocin da suka yi amfani dasu da na’urori da kuma makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.