Isa ga babban shafi

Mali ta ayyana ficewar dakarun majalisar dinkin duniya a karshen shekara

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya ce babu shakka dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya dake kasar zasu kammala ficewa a daidai lokacin da aka tsara, ba tare da Karin wa’adin ba.

dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinki duniya a bakin aiki
dakarun tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinki duniya a bakin aiki AFP - SEYLLOU
Talla

Ministan harkokin wajen Abdoulaye Diop, ya ce tabbas dakarun tabbatar da zaman lafiyar MINUSMA  dake zaune a arewacin Mali zasu kammala ficewa daga kasar zuwa ranar 31 ga watan Disamba ba tare da wata wata ba.

Sai dai Majalisar dinkin duniyar a ranar asabar da ta gabata tace akwai yiwuwar samun jan kafa agame da ficewar ta, saboda fada dake kazanta a yankin arewacin kasar, a yayin da ‘yan tawaye dake dauke da makamai ke barazanar kwace yankin, da zaran dakarun ta sun fice.

Hakanan majalisar ta ce ya zuwa yanzu gwamantin sojin kasar ta Mali bata baiwa dakarun damar kwashe kayakin su daga sassan da suka girke su ba.

Ficewar dakarun wanzar da zaman lafiya ta MINUSMA a karshen shekarar  2023 wani bangare ne na samun tabbatar da sauye sauyen da gwamnatin sojin ke bukatar aiwatarwa, a cewar ministan.

A yanzu haka dai ana cigaba da gwabza kazamin fada a tsakanin dakarun na Mali da gugun ‘yan awaren Tuareg na kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.