Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta fara janyewa daga sansanonin yankin Kidal da ke Mali

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya MINUSMA sun fara ficewa daga sansanonin su guda biyu na Tessalit da Aguelhok da suke aiki a yankin Kidal dake arewacin Mali.

Sojojin MINUSMA yayin gudanar da sintiri a yankin Kidal da ke Arewacin Mali.
Sojojin MINUSMA yayin gudanar da sintiri a yankin Kidal da ke Arewacin Mali. REUTERS/Adama Diarra
Talla

Dangane da ficewar dakarun na Majalisar dinkin duniyar tuni wasu jiragen sojin Mali guda biyu suka sauka a daya daga cikin sansanonin dake Tessalit, yayin da sojojin suka bayyana cewa ‘yan tawaye sun budewa jiragen wuta a yayin da suke kokarin sauka a sansanin.

Daya daga cikin jiragen ya kama da wuta kafin saukar sa, amma babu wanda ya mutu duk da cewa ya sauka a cikin mawuyacin hali, sannan jirgin ya ragargaza wuraren da ‘yan tawayen suka kaddamar da harin akansu.

“Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA sun kwatanta barin wutar da ake yi a matsayin tabarbarewar yanayin tsaro dake barazana ga rayuwar daruruwan sojojinta” kamar yadda mai Magana da yawun sakatare janar na majalisar dinkin duniya Stephen Dujarric ya shaida

.

Dakarun dai sun yi iya kokarin su wajen tabbatar da lumana duk  da tabarbarewae tsaron amma abin ya ci tura.

Yankin arewacin ya kasance fagen fafatawa a tsakanin dakarun gwamnatin Mali da gungun  ‘yan tawaye dake faffutukar samun ‘yantaciyar kasa ta CMA da kuma GSIM wacce ke da alaka da kungiyar  Algaeda.

Dakarun na majalisar dinkin duniya zasu kamala ficewa  ne a ranar 31 ga watan Disamba bayan da suka shafe shekaru suna gudanar da aikin.

Sai dai ficewar tasu ya haifar da tsatssamar gabar a tsakanin bangarorin ‘yan tawaye biyu dake gwagwarmayar kafa kasa mai ‘yanci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.