Wasu masu dauke da makamai sun karbe sansanonin soji 2 arewacin Mali
Wasu mutane dauke da makamai sun kame wani sansanin soji a arewacin Mali a jiya Lahadi, kamar yadda wasu jami’an gwamnatin kasar suka tabbatar, bayan da kungiyar ‘yan tawayen Azbinawa ta dau alhakin harin.
Wallafawa ranar:
A jiya Lahadi rundunar sojin Mali ta tabbatar da aukuwar lamarin a dandalin sada zumunta, inda ta ce da misalin karfe 3 da rabi agogon GMT ne maharan suka afka wa garin Lere da ke yankin Timbuktu na arewacin kasar.
Wata majiya ta ce bayan ba-ta-kashi ne maharan suka kwace sansanin, kuma a halin da ake ciki yana hannunsu.
Wani jami’in gwamnatin yankin ya ce an samu asarar rayuka, said dai har yanzu ba a kai ga tantance adadin wadanda suka mutu ba.
A shekarar 2012 ce ‘yan tawaye Azbinawa masu neman ballewa daga kasar suka kaddamar da hare-hare, kafin daga bisai suka rattaba hannu a yarjejeniyar zaman da gwamnatin kasar a shekarar 2015; sai dai yarjejeniyar na daf da wargajewa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu