Isa ga babban shafi

Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun kulla yarjejeniyar tsaro

Shugabannin kasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar sun sanya hannu a yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro a tsakaninsu, kamar yadda ministotin kasashen uku suka bayyana a yayin wani taron manema labarai a yau Asabar. 

Kyaftin Ibrahim Traoré jagoran mulkin Sojin Burkina Faso.
Kyaftin Ibrahim Traoré jagoran mulkin Sojin Burkina Faso. AFP - ALEXEY DANICHEV
Talla

A cikin wata sanarwa da shugaban gwamnatin sojin Mali Assimi Goita ya wallafa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter, ya ce sun yi wannan hadaka ne don ba su damar samar da kariya ga al’ummarsu. 

Kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar da ke da iyaka da juna sun shafe tsawon shekaru su na fama da matsalar tsaro musamman daga kungiyoyin da ke ikirarin Jihadi. 

Shugaban gwamnatin sojojin kasar Mali Kanal Assimi Goita.
Shugaban gwamnatin sojojin kasar Mali Kanal Assimi Goita. AP - Baba Ahmed

Haka nan dukkanin kasashen 3 sun fuskanci juyin mulki daga tsakanin shekarar 2020 zuwa yanzu, inda Nijar ta kasance kasa ta karshe a cikinsu da ta fuskanci na ta juyin mulkin a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata. 

A lokacin da ministan tsaron Mali Abdoulaye Diop ke yi wa taron manema labarai bayani a Asabar din nan, ya ce hadin gwiwar ta shafi bangaren tsaro da kuma na tattalin arzikin kasashen 3. 

Shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya ce sai nan da shekaru uku masu zwua za su mika mulki ga farar hula.
Shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani ya ce sai nan da shekaru uku masu zwua za su mika mulki ga farar hula. AP

Dukkanin kasashen 3 dai na fuskantar takun-saka yanzu haka da Faransa kasar da ta yi musu mulkin mallaka, lamarin da ya basu damar hade kansu don tunkarar matsalolin da suka dabaibaye su.

Hatta matakin kasashe na katse alaka da Nijar bayan juyin mulkin na watan Yuli, Mali da Burkina Faso kadai ne kasashen da suka nuna mata goyon tare da bata tallafi ta fannoni daban-daban.

Haka zalika dukkanin kasashen 3 yanzu haka na fama da matsalolin tattalin arziki baya ga matsanancin talaucin da ya dabaibaye al'ummarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.