Isa ga babban shafi

Kason farko na sojin Faransa sun isa Chadi daga Nijar

Rundunar sojin Faransa, ta ce kason farko na bataliyar sojojin dakarunta da ta fara janye su daga Jamhuriyar Nijar, a bisa umarnin sojojin da suka yi juyin mulki a kasar, sun isa Chadi, bayan da suka shafe tafiya mai nisan kilomita dubu sama da dubu 1 da 600 cikin kwanaki 9. 

Sojojin Faransa kenan da ke shirin ficewa daga Nijar.
Sojojin Faransa kenan da ke shirin ficewa daga Nijar. © THOMAS COEX / AFP
Talla

 

Yayin zanta wa da kamfanin dillancin labarai na AFP, mai magana da yawun rundunar sojin Faransa Pierre Gaudilliere ya ce bayan sararawa a Chadin, dakarun nasu za su tashi ne kai tsaye zuwa birnin Paris. 

A makon da ya gabata, sojojin Faransar suka fara ficewa daga Nijar, bayan da sojojin da suka yi wa shugaba Bazoum juyin mulki a watan Yuli suka ba su umarnin ficewa. 

Karo na uku kenan cikin watanni 18, da wata kasa da baya Faransar ta yi  wa mulkin mallaka ta kori sojojinta a nahiyar Afirka, lamarin da ya dakushe tasirinta a nahiyar. 

A baya dai dakarun Faransa kimanin dubu 1 da 400 aka rarraba a zuwa sassan Nijar, inda wasu ke birnin Yamai, wasu kuma ke yammacin kasar domin yaki da ‘yan ta’adda masu alaka da kungiyoyin IS da Al Qa’ida. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.