Kotun Gabon ta sallami Mike Jocktane da Thérence Gnembou
A Gabon, an saki wasu daga cikin yan adawa da suka hada da Mike Jocktane da Thérence Gnembou ,da wani mutum da aka kama su tare a lokacin da suka yi kokarin neman shiga kasar Equatorial Guinea.
Wallafawa ranar:
Kotun Gabon ta zartas da hukuncin sallamar wucin gadi a ranar Juma'a 13 ga Oktoba. Wadannan tsoffin 'yan takara a zaben shugaban kasa na baya-bayan nan da suka janye domin bayar da goyan baya ga dan takarar adawa Albert Ondo Ossa.
An cafke su a lokacin da suka yi kokarin isa kasar Equatorial Guinee da nufin isar da sako ga shugabannin kasashe mambobin kungiyar kasashen tsakiyar Afrika.Jim kadan bayan kama su ne sojojin suka kiffar da Ali Bongo Ondimba,wanda hukumar zabe ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben kasar duk da cewa ba shida isasar lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu