Isa ga babban shafi

Mali ta hana kamfanin Air France sake dawo da jigilar fasinja a kasar

Gwamnatin sojin Mali ta soke izinin da ta bai wa kamfanin sufurin jiragen saman kasar Faransa na Air  France na dawo da jigilar fasinja a kasar.

Jirgin kamfanin Air France.
Jirgin kamfanin Air France. © Spaceaero2 / Wikimedia Commons
Talla

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da kamfanin na Air France ya sanar da cewa daga wannan Juma’a zai koma aikin jigilar fasinjoji daga filin tashi da saukar jiragen sama na Charles de Gaulle a Paris, zuwa Bamako babban birnin Mali.

A watanni  biyu da suka wuce ne dai sojojin da ke mulkin Mali suka dakatar da kamfanin daga jigilar fasinja a kasar, sakamakon tankiya tsakninsu da gwamnatin Faransa.

Mahukuntan kamfanin Air France sun tabbatar da soke wannan izinin jigilar fasinjoji da gwamnatin sojin Mali ta yi, suna mai cewa babu wani dalili da ta bayar dangane  da matakin da ta dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.