Isa ga babban shafi

Karfen hakar ma'adanai ya kashe mutane 9 a Zimbabwe

Akalla mutane 9 ne suka mutu a wajen hakar ma’adanai dake birnin Chegutu mai nisan kilomita 120 daga babban birnin kasar Zimbabwe Harare.

Har yanzu dai ana ci gaba da neman wasu mutane fiye da 20 da ba'a  gani ba sanadin ruftawar
Har yanzu dai ana ci gaba da neman wasu mutane fiye da 20 da ba'a gani ba sanadin ruftawar Getty Images/Peter Ptschelinzew
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa wani karfe mai nauyi ne ya balle daga jikin karfe hakar ma’adanan, inda kuma ya hallaka mutane 9 nan take.

Shugaban kamfanin da ke hakar ma’adanai a wajen, Henrietta Rushwaya, ya ce kawo yanzu an samo gawar mutane 4 yayin da ake ci gaba da neman gawar mutane 5 da ake kyautata zaton karfen ya daddatsa sassan jikin su.

Guda daga cikin masu aikin ceto a wajen Hussein Phiri ya ce aikin laluben sassan jikin mutanen na bada wahala, la’akari da yadda ramukan hakar ma’adanan ke ruftawa, abinda ke hana ma’aikata sakin jiki wajen neman mutanen.

Johannes Nyautete guda daga cikin masu aikin hakar ma’adanan da suka tsira, yace bayan karfen ya balle, sai kuma ramin hakar madanan ya rika ruftawa.

Bayanai sun ce mutane 20 ne suka fada cikin ramukan hakar ma’adanan, kuma har kawo yanzu ana neman su ruwa a jallo.

Ministan ma’adanan kasar Soda Zhemu wanda ya kai ziyara wajen da lamarin ya faru ya ce wannan abin takaici ne, yayin da roki masu aikin ceto su kara zage damtse wajen gano mutanen da iyalan suke cikin tashin hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.