Harin 'yan ta'adda ya hallaka mutane 9 a arewacin Ghana
Wani harin kwanton bauna da ‘yan bindiga suka kai yayi sanadin mutuwar mutane 9 a yankin arewacin kasar Ghana.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Guda daga cikin masu rike da sarautar gargajiya na yankin Pusiga da ke arewacin kasar Zubeiru Abdulai ya shaidawa manema labarai cewa harin ya faru ne a wani karamin kauye da ke dab da iyakar kasar da Burkina Faso, inda mayakan da ke ikirarin jihadi ke da karfi matuka.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan ta’addar haye kan babura sun budewa wasu ‘yan kasuwa da ke hanyar su ta zuwa gurin sana’o’in su wuta nan take kuma 9 suka mutu sai wasu da dama da suka jikkata, wadanda yanzu haka ke karbar kulawar likitoci a babban asibitin Bawku.
Jami’an yan sandan yankin ta cikin wata sanarwa da suka fitar, sun ce mafi yawan wadanda lamarin ya rutsa da su mata ne.
Ba’a cika samun rahoton ta’addanci a Ghana ba, sai dai ya zama tamkar ruwan dare a makwaftanta Burkina Faso, Togo da kuma Côte d'Ivoire, kasashen da mayakan da ke ta’addanci da sunan addini suka yi kakagida.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu