Isa ga babban shafi

Nijar: 'Yan ta'adda sun kona motocin kayan abinci a kan iyakar Burkina Faso

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun harbe direba dan kasar Ghana mai tuka wata babbar motar dakon kaya a yayin da yake kokarin fitar da abinci daga Jamhuriyar Nijar. 

Manyan motoci yayin da suka yi jerin gwano akan iyakar Najeriya da Nijar.
Manyan motoci yayin da suka yi jerin gwano akan iyakar Najeriya da Nijar. © Daily Trust
Talla

Maharan da ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne, ba wai kawai sun far wa ayarin motocin ba ne, sun kuma kona manyan motoci da dama.

A halin yanzu direban da ya jikkata yana jinya a wata cibiyar lafiya a Nijar.

Ya kasance cikin rukunin direbobin da suka zabi hanyar Burkina Faso don kai kayan abinci masu mahimmanci zuwa Ghana.

Matakin ya biyo bayan rufe iyakokin kasar ta Nijar ne sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi, lamarin da ya janyo takun-saka da kungiyar ECOWAS.

Rahotanni na cewa, direbobin sun yi yunkurin wuce iyakar Burkina Faso ne da kansu, bayan da suka jira a yi musu rakiya.

Rikicin da ya biyo bayan hambarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka yi a baya-bayan nan ya jefa Nijar cikin wani yanayi na rashin tabbas.

Wannan hargitsin siyasa ya yi matukar kawo cikas ga zirga-zirgar kayayyaki da na jama'a zuwa ko kuma fita daga kasar da ke yammacin Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.