Isa ga babban shafi

Ghana ta tisa keyar 'yan Nijar da ke bara a titunan Accra zuwa gida

Gwamnatin Ghana ta sanar da tisa keyar bakin haure ‘yan kasar Nijar da ke bara a titunan babban birnin kasar Accra su akalla dubu 1 da 300 da 20 zuwa kasarsu ta asali cikin watan da mu ke na Yuni.

Ghana ta bi sahun Senegal wajen taso keyar mabarantan na Nijar.
Ghana ta bi sahun Senegal wajen taso keyar mabarantan na Nijar. © RFI Mandenkan/ Mohamoud Kaba DIAKITE
Talla

Sanarwar da ma’aikatar kula da zamantakewa da kare kananan yara ta fitar ta ce an samu wadanda aka maida kasarsu ne a titunan birnin Accra da kuma karkashin gadoji suna garararamba da yawon bara.

Sanarwar ta ci gaba da cewa daga cikin wadanda aka tisa keyarsu zuwa gida akwai maza 300, mata 400 da yara 620, kuma an maida su ne a tsakanin ranakun 7 da 8 ga watan yuni.

Ma’aikatar, wadda ta gudanar da aikin aikewa da wadeannan mutane gida da hadin gwiwar gwamnatin Nijar,  ta ce akwai kaduwa ganin cewa yara kanana na gararamba a gari, inda suke jefa rayuwarsu cikin hatsari.

Wata kungiyar kare hakkin yara kanana ta kasa da kasa ta yaba da matakin gwamnatin Ghana, ta na mai cewa ana yi ne don taimakawa yara.

Ofishin jakadancin Nijar a birnin Accra ya ce gwamnati za ta tallafa wa wadanda aka tisa keyarsu zuwa gida da abin da za su dafa don zaman gari, sai dai bai yi wani karin bayani a kan hakan ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.