Isa ga babban shafi

Harin ta'addanci ya kashe sojoji da fasinjojin kwale-kwale 64 a Mali

Rundunar sojin Mali ta ce, wasu da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi ne sun kai farmaki kan sansanin sojoji da wani jirgin ruwan fasinja a kogin Neja da ke arewacin kasar ranar Alhamis, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 64.

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a yankin Timbuktu dake kasar  Mali, watan Satumbar 2021
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a yankin Timbuktu dake kasar Mali, watan Satumbar 2021 © Moulaye Sayah/AP
Talla

Hare-haren biyu maban-banta, an kai su ne kan wani jirgin ruwan Timbuktu a kan kogin Neja da kuma wani sansanin sojoji a Bamba da ke arewacin yankin Gao.

Sakamakon farko sun tabbatar da mutuwar fasinjojin kwale-kwalen 49 da kuma sojoji 15.

Sanarwar gwamnatin rikon kwaryar soji ta ce, ‘yan ta’addan sun kai farmaki kan jirgin ruwan fasinjan na kamfanin Comanav ne da misalin karfe 11:00 na safiyar Alhamis a yankin Gourma-Rharous. 

Yayin da wata sanarwar ta daban kuma, kamfanin na Comanav ya ce, an kai wa jirgin ruwan na shi hari ne da makaman roka akalla uku, yayin da yake kan jigila a tsakanin garuruwan da ke bakin kogin na Neja. 

Tuni kungiyar da ke ikirarin jihadi a arewacin kasar da ke da alaka da Al-Qaeda ta dauki alhakin kai harin.

Kungiyar da tun farko ta sanar da datse duk wata hanya da ke shiga birnin Timbuktu a arewacin Mali. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.