Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta kama wasu sojoji 3 da ke yunkurin kifar da gwamnatin Traore

Mahukuntan Burkina Faso sun kame wasu sojoji 3 da ke zagon kasa ga gwamnatin sojin kasar karkashin jagorancin kyaftin Ibrahim Traore.

Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore.
Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Ibrahim Traore. © AFP
Talla

Ofishin babban mai shigar da kara na Burkina Faso ya ce sojojin wadanda suka kunshi guda da ya yi ritaya da kuma wadanda ke bakin aiki, na da manufar wargaza gwamnatin mulkin Sojin kasar.

Sanarwar da Ofishin ya fitar a yau juma’a ya bayyana cewa, bayan dogon binciken da aka gudanar ya gano yadda sojojin 3 wadanda dukkaninsu ke aiki a sashen tattara bayanan sirri, suka shafe tsawon lokaci su na aikin laluben bayanai na musamman kan kusoshin gwamnatin Sojin kasar ciki har da kyaftin Traore.

Sanarwar ta ce sojojin 3 na bibiyar wuraren da Traore ya sanya kafa dama gidanshi baya ga gidajen makusantanshi, a wani yunkuri na wargaza gwamnatin rikon kwaryar da ke fatan dakile matsalolin tsaron da kasar ke fama da su.

Sanarwar ta ce dogon binciken da aka gudanar ne ya kai ga nasarar kame sojojin  3 kuma yanzu haka suna tsare don amsa tambayoyi game da wadanda suke yi wa aiki.

Sojojin 3 da aka bayyana sunayensu da Windinmalegde Kabore da Sajan Brice Ismael Ramde da kuma Sami Dah mai ritaya, babban mai shigar da kara na Burkina Faso Majo Alphonse Zorma ya ce za su fuskance tuhume-tuhumen yunkurin kifar da gwamnati karya dokokin Soja baya ga kalubalantar tsaron kasa sai kuma yunkuri jefa rayuwar jama’a a hadari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.