Isa ga babban shafi

Kungiyar JNIM ta dauki alhakin kashe sojojin Burkina Faso fiye da 50

Kungiyar JNIM mai alaka da Al Qa’eda, ta dauki alhakin harin da aka kai a yankin Yatenga da ke Burkina Faso, inda ‘yan ta’adda suka kashe jami’an tsaro fiye da 50. 

'Yan ta'addar da ke da alaka da Al-Qaeda sun dauki alhakin kashe sojojin Burkina Faso fiye da 50.
'Yan ta'addar da ke da alaka da Al-Qaeda sun dauki alhakin kashe sojojin Burkina Faso fiye da 50. U.S. Africa Command - Sgt. Benjamin Northcutt
Talla

 

A ranar Talata rundunar sojin Burkina Faso ta sanar da kashe mata dakaru 17 tare da wasu jami’an tsaron na ‘yan sa-kai 36, yayin kazamin artabun da suka yi da ‘yan ta’addan a arewacin kasar. 

Farmakin shi ne mafi muni cikin watannin baya bayan nan da aka gani a kasar, da ta shafe shekaru kusan 10 tana fama da hare-haren ta’addancin da suka bayyana tun shekarar 2015. 

Matsalar tsaron ta yi kamari a shekarar nan, lamarin da ke ci gaba da yin tasiri kan makwaftanta, wato Mali da Jamhuriyar Nijar, inda a jumlace rayukan dubban mutane suka salwanta, wasu miliyoyin kuma suka tsere daga muhallansu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.