Isa ga babban shafi

Sojojin Burkina Faso sun kashe 'yan ta'adda 40 a wata arangama

Jami'an 'yan sandan Burkina Faso biyar ne suka mutu a wani hari da aka kai a tsakiyar gabashin kasar, inda akalla 40 daga cikin maharan suka kwanta dama a lokacin da mahukuntan kasar suka kaddamar da wani farmaki, in ji rundunar sojin kasar.

Mayakan sa kai kenan daga yankin Gatia a Burkina Faso
Mayakan sa kai kenan daga yankin Gatia a Burkina Faso © SOULEYMANE AG ANARA / AFP
Talla

Harin ya afku ne da yammacin ranar Asabar lokacin da aka kai hari kan jami’an rundunar ‘yan sanda a kusa da Diougo-Yourga, dake lardin Koulpelogo kusa da kan iyakar Togo, in ji rundunar.

Sanarwar ta kara da cewa, harin ya janyo asarar rayukan jami'an 'yan sanda biyar. 

Yayin mayar da martani ne, jami'an tsaron suka kashe ‘yan ta’adda akalla arba’in tare da kwace makamansu.

A ranar 7 ga watan Agusta ne aka sake kai wani mummunan hari a Koulpelogo, inda aka kashe mutane kusan ashirin a Nohao da ke kusa da garin Bittou, a cewar majiyoyin tsaro.

A tsakiyar watan Yuli, shugaban rikon kwarya na Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traore, wanda ya kwace mulki a watan Satumban 2022, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula, yana mai cewa masu tayar da kayar baya suna wuce gona da iri..

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.