Isa ga babban shafi

Daga nan zuwa kowanne lokaci za mu iya kutsawa Nijar - ECOWAS

Kungiyar ECOWAS ta amince da matakin karshe na yuwuwar amfani da karfin soji don maido da dimokuradiyya a Nijar bayan hambarar da shugaban kasar Mohammed Bazoum tare da tsare shi a watan jiya.

Galibin kasashe 15 na kungiyar ECOWAS sun shirya tsaf domin bayar da gudumawarsu ga rundunar hadin gwiwa.
Galibin kasashe 15 na kungiyar ECOWAS sun shirya tsaf domin bayar da gudumawarsu ga rundunar hadin gwiwa. REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta amince a ranar Juma'a cewa za ta fara aiki da rundunar tsaro a matsayin mataki na karshe idan yunkurin diflomasiyya ya ci tura, ba tare da bayyana lokacin da hakan zai faru ba.

"A shirye muke mu shiga kasar a duk lokacin da aka ba da wannan umarni," in ji kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS Abdel-Fatau Musah yayin bikin rufe taron yini biyu na hafsoshin sojojin Afirka ta Yamma a Accra babban birnin kasar Ghana.

“An kuma yanke ranar karshe na shiga kasar. Mun riga mun amince kuma mun daidaita abubuwan da za a bukata don shiga tsakani,” in ji shi, yana mai jaddada cewa ECOWAS na neman yin sulhu cikin lumana da shugabannin sojojin Nijar.

Manyan hafsoshin tsaron kungiyar sun gana don daidaita bayanan yuwuwar aikin soji na maido da Bazoum idan har tattaunawar da ake yi da jagororin juyin mulkin suka ci tura.

Yawancin kasashe mambobin kungiyar ECOWAS 15 a shirye suke su ba da gudummawar rundunar hadin gwiwa, in ban da Cape Verde da kuma wadanda ke karkashin mulkin soja - Mali, Burkina Faso da Guinea kamar yadfda wani jami'in kungiyar ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.