Isa ga babban shafi

Zamu mayar da mulkin farar hula ta ko wacce hanya - Hafsoshin ECOWAS

Hafsoshin sojin kasashen Afirka ta Yamma da ke taro a birnin Accra ta kasar Ghana sun ce ECOWAS za ta mayar da mulkin farar hula a Jamhuriyar Nijar ta ko wacce hanya. 

Wani bangare na kwamitin tsaron ECOWAS a taronsu kan Nijar a birnin Accra na kasar Ghana.
Wani bangare na kwamitin tsaron ECOWAS a taronsu kan Nijar a birnin Accra na kasar Ghana. REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

Yayin da yake jawabin bude taron hafsoshin, wanda shi ne karo na biyu da suke yi domin nazari a kan matakan da ya dace a dauka wajen amfani da karfi a kan sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar, kwamishinan tsaro da zaman lafiya, Abdul Fatau Musah ya ce abin da ke gabansu shi ne ganin an dawo da mulkin farar hula a kasar. 

Shugabannin kungiyar ECOWAS suka bai wa hafsoshin sojin kasashensu umarnin nazari da kuma bada shawara a kan matakan da ya dace a dauka idan bukatar amfani da karfin soji ya yi, sakamakon bijirewar sojojin da suka yi juyin mulkin. 

Ministan Tsaron Ghana, Dominic Nitiwul tare da manyan hafsoshin tsaron Kungiyar ECOWAS a birnin Accra a wannan Alhamis.
Ministan Tsaron Ghana, Dominic Nitiwul tare da manyan hafsoshin tsaron Kungiyar ECOWAS a birnin Accra a wannan Alhamis. © Francis Kokoroko, Reuters

Wannan matsayi na shirin amfani da karfin na ci gaba da fuskantar adawa daga wasu kasashe da kuma kungiyoyin jama’a ciki har da Amurka da Rasha wadanda ke bukatar ci gaba da daukar matakan diflomasiya domin warware matsalar. 

Rahotanni sun ce, taron kungiyar kasashen Afirka ta AU a kan juyin mulkin na Nijar bai kai ga daukar matsayin bai-daya ba sakamakon rarrabuwar kawunan da aka samu tsakani kasashen da suka halarci taron. 

Firaministan da sojojin Nijar suka nada Ali Lamine Zeine ya ce tuni suka fara shirin mayar da mulki a kasar, yayin da majiyoyi da dama ke cewa, sojojin sun bayyana bukatar tattaunawa da kungiyar ECOWAS. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.