Isa ga babban shafi

Kasashen Afrika sun kasa cimma matsaya kan Jamhuriyar Nijar

A yayin da hankulan kasashen duniya suka karkata kan Jamhuriyar Nijar, ana ci gaba da dakon Kwamitin Tsaro da Zaman Lafiya na Tarayyar Afrika da ya fitar da sanarwar bayan taron da ya gudanar a ranar Litinin da ta gabata duk da cewa, ana zaton ya gaza cimma matsaya guda.

Hoton Ofishin kungiyar tarayyar Afrika a birnin Addis-Abeba, babban birnin kasar Etchiopia le 29 janvier 2017. REUTERS/Tiksa Negeri - RC1D016AA660
Hoton Ofishin kungiyar tarayyar Afrika a birnin Addis-Abeba, babban birnin kasar Etchiopia le 29 janvier 2017. REUTERS/Tiksa Negeri - RC1D016AA660 REUTERS - Tiksa Negeri
Talla

Batutuwan da su ka shafi takunkumai  da kuma aniyar amfani da karfin soja  da kungiyar kasshen yammacin nahiyar Afrikia ECOWAS ko CEDEAO ta bijiro da su  kan Nijar ba su samu amincewar wani bangare na  mambobin kwmitin ba, kamar yadda jami’an diflomasiya su ka sanar wa RFI.

Mawuyaciyar tattaunawa ce mai tsawo kuma  ba  tare da nukunuku ba aka gudanar, inda  jami’an diflomasiyar na nahiyar Afrika suka bayyana cewa, yanzu haka,  kasashe mambobin Kungiyar Tarayyar Afrika,  sun lura da mawuyacin halin da kasashen nahiyar ke ciki, Inda aka gudanar da juye-juyen mulkin soji har 6 a kasa da  shekaru 3 da suka gabata a nahiyar,  kamar yadda majiyar ta ambato.

Majiyar ta kara bayyana cewa, yanzu haka ana fuskantar wani irin mawuyacin hali ne da dokokin da ake da su, ba su iya magancewa, a yayin da kwamitin samar da zaman lafiyar na Tarayyar Afrika  ke cewa, lamarin ya kasance wani mawuyacin abu ne a gare ta.

Majiyar ta ce ruhin tattaunawar ya karkata ne  kan matsayin da Kungiyar ta Tarayyar Afrika za ta dauka ne, dangane da matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka kan son yin amfani da karfin soji kan sojojin da suka hambarar da shugaban farar hula a  kasar ta Nijar.

Wasu mambobin  Kwamitin Zaman Lafiyar da Tsaro, sun zabi  hanyar  taka-tsan-tsan ne ta hanyar neman karin haske kan matakin da kungiyar ta ECOWAS ta dauka da zai kai ta ga yin  amfani da karfin soja wajen mayar da halastaciyar  gwamnatin farar hular kasar.

Yanzu haka dai tun ranar 14 ga watan Agustan da muke ciki ne,  kasashe mambobin kwamitin na CPS ke tattauna matsalar ta Nijar, inda ake sa ran su fitar da sanarwar bayan taron dangane da matsayinsu,  kan matakin da  ECOWAS ke shirin dauka na amfani da karfin soji a Jamhuriyar Nijar.

Daga nasa bangaren, daya daga cikin jami’an diflomasiyar nahiyar Afrika da ya halarci  zaman taron ya bayyana cewa,  kasashen yankin gabashi da arewacin nahiyar Afrika, sun tsaya kai da fata, cewa ba su amince da yin amfani da karfin soji kan sojin juyin mulkin na Nijar domin kawar da su, matakin da ke tattare da mummunan hadari.

A cewar majiyar, kasashen tsakkiyar Afrika, sun bayyana rashin amincewarsu da yin amfani da karfin soji.

A yayin da aka kawo  karshen zaman taron tun ranar Litanin, har yanzu an kasa karanta sanarwar bayan taron, shiru kake ji, a cewar  majiyar.

Kasashen mambobin Kwamitin Zaman Lafiyar Kungiyar Tarayyar Afrika dai, tun ranar 14 ga wannan watan Agusta ne,  suka kawo karshen tattaunawar tasu,  kan matakin da ya kamata a yi amfani da shi, kan sojojin juyin mulkin Nijar, lura da muhimmancin da batun ya ke da shi  in ji majiyarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.