Isa ga babban shafi

Faransa da Mali sun dakatar da bayar da biza ga 'yan kasashensu

Kasashen Faransa da Mali sun dakatar da bayar da biza ga 'yan kasashen biyu, sakamakon wasu dalilai.

Wani sashe na filin jirgin saman Roissy-Charles-de-Gaulle na kasar Faransa kenan, da ke Arewacin Paris.
Wani sashe na filin jirgin saman Roissy-Charles-de-Gaulle na kasar Faransa kenan, da ke Arewacin Paris. AFP - KENZO TRIBOUILLARD
Talla

A cikin wata sanarwa da aka wallafa a X wato Twitter, ma'aikatar harkokin wajen Mali ta ce za ta dakatar da bayar da biza ga 'yan kasar Faransa a ofishin jakadancinta da ke birnin Paris a wani mataki na mayar da martani.

Wannan sanarwa ta biyo bayan matakin Faransa, yayin da ofishin jakadancin Faransa ya dakatar da bayar da biza a Bamako babban birnin kasar Mali.

Wannan babban mataki da Faransa tace an yi shi ne saboda tsaro, ya haifar da sake tsara ayyuka a ofishin jakadancinta, wanda ke nufin ba zai iya ba da biza ba har sai lokacin da hali yayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.