Isa ga babban shafi

ECOWAS ta yi amfani da karfin Soji a kasashe 6 kafin Nijar - Alkaluma

Dai dai lokacin da hankula suka ta shi bayan matakin kungiyar ECOWAS na shirin amfani da karfin Soji wajen dawo da mulkin farar hula a jamhuriyyar Nijar, wasu alkaluma sun tattaro yadda kungiyar a baya ta yi amfani da karfin wajen dawo da demokradiyya a wasu kasashe har guda 6 na nahiyar Afrika.

Taron kungiyar ECOWAS a Abuja babban birnin Najeriya.
Taron kungiyar ECOWAS a Abuja babban birnin Najeriya. AFP - KOLA SULAIMON
Talla

Tun shekaru 32 da suka gabata kungiyar ECOWAS ta fara amfani da karfin Soji wajen tabbatar da dawowar mulkin Demokradiyya a kasashe, inda a shekarar 1990 kungiyar mai mambobi 15 ta hada wata runduna ta musamman mai kunshe da dakaru kusan dubu 20 galibi sojin Najeriya wadanda suka yi yaki a Liberia da nufin kawo karshen yakin basasar da kasar ta fada, wanda zuwa shekarar 1997 suka yi nasarar mayar da kasar karkashin mulkin demokradiyya bayan gudanar da zabe.

A 1997 ECOWAS ta sake aikewa da dakaru Saliyo wadanda suka kawar da sojojin da suka yi juyin mulki tare da mayar da shugaba Ahmad Tejan Kabbah kan kujerarsa inda a shekarar 1999 suka sake fatattakar ‘yan tawayen kasar gabanin majalisar dinkin duniya ta ja ragamar aikin wanzar da zaman lafiya a kasar a shekarar 2000.

Cikin 1999 ECOWAS ta aike da dakaru Guinea Bissau bayan soji sun hambarar da gwamnatin Joao Bernado Vieira, yayinda ko a Ivory Coast cikin shekarar 2003 aka ga dakarun kungiyar dubu 1 da 300 don dakile yakin basasar kasar.

Haka zalika a 2013, ECOWAS ta aike da dakaru Mali don yaki da ‘yan tawaye gabanin kare aikin rundunar cikin watan Yunin da ya gabata.

Bugu da kari anga dakarun ECOWAS a Gambia cikin shekarar 2017 lokacin da Yahya Jammeh ya ki amincewa da sauka daga mulki don hawan zababben shugaba Adama Barrow.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.