Isa ga babban shafi

Sudan ta Kudu: Shugaba Salva Kiir ya kori ministan kudin kasar

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya kori ministan kudi Dier Tong Ngor, a wani ab una sabon sauyin majalisar ministocin kasar da ke gabashin Afirka na ba zato ba tsammani, amma mai magana da yawun Kiir ya alakanta matakin da koma bayan tattalin arzikin kasar da aka samu.

Shugaba Salva Kiir na kasar Sudan ta Kudu kenan.
Shugaba Salva Kiir na kasar Sudan ta Kudu kenan. AP - Gregorio Borgia
Talla

Kudin kasar Sudan ta Kudu ya fuskanci ya fadi da kusan kashi daya bisa uku idan aka kwatanta da dala a cikin watanni biyun da suka gabata, inda masu sharhi suka ce abubuwan da suka durkusar da ita sun hada da tabarbarewar tattalin arziki sakamakon rikicin kabilanci da kuma gazawar Kiir wajen bin yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2018.

Daga shekarar 2020 zuwa yanzu dai, Salva Kiir ya kori ministocin kudi hudu.

A watan Maris ya kori ministan harkokin wajen kasar ba tare da wani bayani ba, kasa da mako guda bayan korar ministocin tsaro da na cikin gida wanda hakan kuma ya saba wa yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan adawa.

Tattalin arzikin kasar dai ya dogara ne kan sayar da danyen mai amma yakin basasar da ya barke a tsakanin shekarun 2013-2018 jim kadan bayan samun 'yancin kai daga Sudan a shekara ta 201, ya jefa kasar cikin rudani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.