Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

An saki 'yan jaridar da suka yada hoton shugaba Salva Kiir na fitsari a wando

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta saki wasu ‘yan jaridu guda biyu da aka tsare saboda yada bidiyon da ke nuna shugaban kasar Salva Kiir ya na fitsari a cikin wandonsa lokacin wani biki. 

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu.
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu. AFP
Talla

Su dai wadannan ‘yan jaridu 2 na daga cikin guda 7 da aka kama a watan janairu kamar yadda kungiyar ‘yan jaridun Sudan ta kudu ta sanar. 

An kama wadannan ‘yan jaridu guda 2 da ke aiki a kafar yada labaran gwamnati lokacin da aka yada faifan bidiyon da ya haifar da cece kuce. 

Bidiyon ya nuna yadda shugaba Kiir sanye da bakaken kayan da ya saba sawa na fitsari a tsaye a cikin jama’a lokacin da ya ke kaddamar da aikin gina hanya. 

Shugaban kungiyar ‘yan jaridun kasar Patrick Oyet ya bayyana matukar damuwarsu dangane da lamarin, musamman ganin yadda aka tsare ma’aikatan yada labaran na dogon lokaci sabanin abinda doka ta tanada. 

A watan janairu, kungiyar kare hakkokin ‘yan jaridu ta duniya ta bukaci sakin wadannan ‘yan jaridu ba tare da bata lokaci ba, yayin da ta koka akan yadda ake tirsasawa maneman labaran da ke gudanar da aikin su dai dai da tanadin doka.

Jami’in kungiyar da ke kula da yankin Afirka da ke kudu da Sahara, Muthoki Mumo ya ce irin wuce gona da irin da jami’an tsaro ke yi na barazana ga aikin jaridar da kuma ma’aikatansa baki daya. 

Sudan ta kudu na matsayi ta 128 a cikin jerin kasashen duniya 180 da ke musgunawa ‘yan jaridu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.