An yi harbe-harbe cikin dare a birnin Ouagadougou na Burkina Faso
Bayanai daga Burkina Faso na cewa na jiyo karar harbe-harbe a tsakiyar birnin Ouagadougou gab da barikin sojin sama.
Wallafawa ranar:
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa an fara jiyo harbin ne tun da misalin karfe 12:42 na tsakar daren jiya, abin da ake hasashen cewa ya yi kama da yunkurin juyin mulki.
Wannan dai na zuwa ne bayan watanni 10 da juyin mulki kuma karo na biyu a kasa da shekara guda a kasar ta yammacin Africa mai fama da ayyukan ta’addanci.
Har yanzu dai babu wani sahihin labari game da dalilin harbe-harben da ya taso daga gab da barikin sojoji.
Idan mai saurare zai iya tunawa Kyaftin Ibrahim Traore ya hambarar da gwamnatin Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda shima kwace mulkin ya yi daga hannun Roch Marc Christian Kabore a watan Janairun 2022.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu