'Yan Burkina Faso sun gudanar da gangamin neman sabon kundin tsarin mulki
Dubban mutane ne suka yi gangami a kan titunan birnin Ouagadougou na Burkina Faso a ranar Asabar don nuna goyon baya ga sojojin da ke mulkin kasar daa rikicin ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi ya dabaibaye, inda suka mika bukatar sabon kundin tsarin mulki.
Wallafawa ranar:
Masu gangamin sun taru ne a tsakiyar babban birnin na Burkina Faso, duk kuwa da ruwan sama mai kamar da bakin kwarya da aka yi.
Gamayyar kungiyoyin fararen hula ta kasar, wadda a karkashinta akwai sama da kungiyoyi 20 ce ta shirya wannan gangami.
Masu zanga –zangar suna ta wakokin nuna goyon baya ga batun samar da sabon kundin tsarin mulki, tare da yin tir da abin da suka kira manufar Faransa ta bata wa Burkina Faso suna.
Suna ta daga tutocin Mali da Guinea, wato kasashe biyu, wadanda su ma sojoji ne ke jan ragamarsu.
Tun a shekarar 2015 ce Burkina Faso ke fama da matsalar kungiyoyin ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi, wadandaa suka kashe mutane da dama, tare da daidaita al’umma dayawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu