Isa ga babban shafi

Gobarar dajin da ta kone dazuka a Algeria ta bazu zuwa Tunisia

Jami’an kashe gobara a Algeria sun samu nasarar  shawo kan wutar dajin da ta tafka mummunar barna a wasu sassan yankin gabar tekun Meditaraniya, inda aka samu hasarar rayukan mutane akalla 34.

Yadda wutar daji ta kone ababen hawa a garin Bejaia da ke kasar Algeria.
Yadda wutar daji ta kone ababen hawa a garin Bejaia da ke kasar Algeria. © REUTERS/Ramzi Boudina
Talla

Gobarar dajin ta tashi ne a wasu larduna da dama na kasar Aljeriya tun a ranar Litinin, inda ta kone dazuka, da itatuwan zaitun da kuma kananan ciyayi.

Bayanai sun ce jami’an kashe gobara sama da 8,000 ne suka yi aikin shawo kan wutar dajin da ta mamaye wasu yankunan kasar takwas a ranar Talata, da suka hada da Skikda, Jijel, Bouira, Bejaia, Tebessa, Medea, Setif, da kuma El Tarf.

Tuni dai iska mai karfi ta yi sanadin bazuwar wutar dajin daga Algeria zuwa makwafciyarta Tunisia, lamarin da ya tilasta rufe wasu sassan iyakar kasashen biyu.

Yanayin tsananin zafin da ba a taba gani irinsa ba ya haifar da matsaloli a sassan duniya, inda zafin ya kai kololuwa a kasashen China da Amurka da Kudancin Turai da Arewacin Afirka, lamarin da ya janyo aukuwar iftila’in tashin wutar daji.

A kasar Girka daruruwan jami’an kashe gobara ne suka shafe makon da ya gabata suna kokarin kashe wutar da ta rika kone dazukan sassan kasar, lamarin da ya tilasta wa mutane fiye da dubu 30 tserewa daga gidajensu, baya ga dubban masu yawon bude idon da aka kwashe daga wuraren shakatawa da dama da wutar ke yi wa barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.