‘Yan Sandan Brazil sun ceto wasu ‘yan Najeriya matafiya a gabar teku
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce an ceto wasu matafiya hudu a kudu maso gabashin gabar tekun Brazil bayan shafe kwanaki 13 a tekun.
Wallafawa ranar:
Mutanen sun boye ne a wani daki da ke wani bangare na jirgin dake kan hanyarsa na zuwa Brazil.
Ma’aikatan jirgin ruwan dake dauke da tutar kasar Laberiya ne suka same su, wanda ya taso daga Legas a ranar 27 ga watan Yuni.
Wani jami'in 'yan sanda ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa mutanen hudun suna cikin koshin lafiya.
A cewar ‘yan sandan, ‘’yan sandan sun ceto mutanen da suka bayyana cewa su ‘yan Najeriya ne, amma ba su da wata takarda da ke tabbatar da asalinsu.
Sanarwar ta ce mutanen za su ci gaba da kasancewa a hannun Brazil har sai an mayar da su kasarsu ta asali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu