Isa ga babban shafi

Shugaba Raissi na Iran ya caccaki kasashen yammacin Duniya

Shugaban kasar Iran Ebrahim Raissi a ziyara da ya kai kasar Uganda ya bayyana  damuwa ganin rawar da kasashen yammaci ke takawa a siyasar su da kasashen Afirka.

Shugaban kasar Iran  Ebrahim Raïssi
Shugaban kasar Iran Ebrahim Raïssi AP - Vahid Salemi
Talla

Shugaban na Iran Ebrahim Raissi da zai kai ziyara a wasu kasashen Afirka da suka hada da Uganda da Zimbabwe da Kenya ya yaba da kokarin hukumomin kasar Uganda na haramta auren jinsi.

Kasar Ugnada a karkashin Shugabancin  Yoweri  Museveni ta aiwatar da dokoki na hukunta duk mutane dake ra’ayin auren jinsi tare da fuskantar dauri a gidan yari.

Shugaban na Iran ya bayyana goyan bayan sa ga hukumomin kasar ta Uganda,kasar Iran ta dau alkawalin taimakawa wajen gina matatar mai da kasar Uganda ta sanar a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.