Isa ga babban shafi

Za mu kawo karshen juyin mulki a Yammacin Afirka - Tinubu

Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS, ta sha alwashin kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye tsarin mulkin dimokradiyya a nahiyar.

Sabon shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Najeriya kenan, Bola Ahmed Tinubu.
Sabon shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Najeriya kenan, Bola Ahmed Tinubu. © premiumtimes
Talla

Sabon shugaban kungiyar kuma shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya bayyana hakan a Bissau, yace lokaci ya yi da shugabannin yankin za su tunkari matsalolin da ke haifar da juyin mulki a kasashen yankin.

Kungiyar mai mambobin kasashe 15, ta fuskanci juyin mulki har sau biyar a kasashe uku mambobinta tun daga 2020.

“Ba tare da mulkin dimokradiyya ba, babu gwamnati, babu ‘yanci, babu doka. Ba za mu lamunci juyin mulki a yankin Yammacin Afirka ba” in ji Tinubu.

Shugaban na ECOWAS, ya kuma yi gargadi game da barazanar da ke tunkarar yankin, kama daga matsalolin masu tayar da kayar baya, da kuma yadda sojoji ke kwace mulki a wasu kasashen.

Ya ce, matsalar masu dauke da makamai da sauran kalubalen da suka shafi tsaro sune ummul-aba’isin samar da koma baya ga nahiyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.