Isa ga babban shafi

AU ta fara janye sojojinta daga Somalia

Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka a Somaliya, ta ce ta kammala kwashe kashi na farko na dakaranta, a kokarin rage yawan su da take yi da nufin mayar da al’amuran tsaro a hannun sojoji da 'yan sandan kasar. 

Dakarun Sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afrika a Somalia.
Dakarun Sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afrika a Somalia. © Feisal Omar / Reuters
Talla

A cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, an mika jimillar sansanoni 7 ga jami'an tsaron Somaliya, lamarin da ya ba da damar janye dakaru 2 a wa'adin ranar 30 ga watan Yunin da ya gabata. 

A ranar Talatar da ta gaba ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya sake sabunta wa’adin watanni shida ga rundunar ta AU, wacce ke da wa’adin karshen watan Satumba don kara kwashe sojoji dubu 3. 

Rundunar ta AU da ke da jami’an tsaro na sojoji da ‘yan sanda sama da dubu 19 a Somaliya, da suka fito daga kasashen Burundi da Habasha da Kenya da kuma Uganda, nan da karshen shekara mai zuwa  ake saran ta kammala kwashe su daga kasar.

Kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke da alaka da Al-Qaeda na ci gaba da kai hare-hare babban birnin kasar Mogadishu, duk kuwa da hare-haren da sojojin gwamnati da ke samun goyon bayan sojojin kungiyar AU da kuma Amurka suka kaddamar a watan Agustan da ya gabata.

A wani harin da ‘yan kungiyar Al-Shabaab suka kai a karshen watan Mayun daya gabata, a wani sansanin sojojin kungiyar AU da ke kudu maso yammacin babban birnin kasar, sai da suka kashe sojojin Uganda da ake aikin wanzar da zaman lafiya 54.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.