Gwamnatin Libya ta ce ba ta da hannu a harin da aka kai sansanin Wagner
Gwamnatin Libya mai samun goyon bayan kasashe ta ce ba ta da hannu a harin jirgi mara matuki da aka kai wani sansanin dakarun sojin hayar Wagner a gabashin kasar.
Wallafawa ranar:
Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa a ranar Alhamis, wani jirgi mara matuki da ba a tantance asalinsa ba ya kai farmaki a sansanin sojin saman al-Kharrouba mai nisan kilomita 150 daga kudu maso gabashin birnin Bengazi, inda aka yi amannar sansani ne na dakarun Wagner.
Wasu kafofin yada labarai na intanet sun danganta harin da sojin gwamnatin Libya da ke samun goyon bayan majalisar dinkin duniya, wadda abokiyar hamayyarta ta gabashin kasar ke ja da halarcinta.
Gwamnatin mai mazauni a birnin Tripoli ta bayyana mamakin a kan wannan rahoto, inda ta ce ba ta da hannu a ta’asar da Alhamis, hasali ma tana girmama yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Oktoban 2020.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu