Isa ga babban shafi

Kungiyar agaji ta Red Cross, ta ce ta yi nasarar karbo sojojin Sudan 125 daga hannu mayakan RSF

Kungiyar bayar da agajin jinkai ta duniya Croix-Rouge a jiya alhamis ta bayyana cewa ta taka mihimmiyar rawa wajen gaanin mayakan rundunar kai daukin gaggawa RSF a kasar Sudan ta saki sojojin kasar 125 da ta ke tsare da su, gungun dakarun dake ci gaba da yakar sojojin sudan tun cikin watan Avrilun da ya gabata.

Un homme marche pendant que la fumée monte au-dessus des bâtiments après un bombardement aérien, lors d'affrontements entre les Forces paramilitaires de soutien rapide et l'armée à Khartoum Nord, Soudan, le 1er mai 2023.
Un homme marche pendant que la fumée monte au-dessus des bâtiments après un bombardement aérien, lors d'affrontements entre les Forces paramilitaires de soutien rapide et l'armée à Khartoum Nord, Soudan, le 1er mai 2023. REUTERS - MOHAMED NURELDIN ABDALLAH
Talla

Wani labarin kuma na cewa,  an samu wata fashewa mai karfi a kusa da hedkwatar sojojin Sudan, da aka jiyo kararta a ko ina cikin fadin birnin Khartoum, a cewar mazauna birnin.

Kwanaki biyu da gudanar da shagulgulan sallar Layya, yanzu haka ana ci gaba  da tafka kazamin fadan, dake ci gaba da lakume rayuka tun bayan barkewarsa a watan avrilun da ya gabata, tsakanin sojojin na Sudan da kuma na gungun mayakan rundunar kai daukin gaggawa ta RSF, al’amarin da  ya tilsata wa miliyoyin mazauna birnin Khartum tserwa zuwa kasashe makwafta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.