An yi luguden wuta a babban birnin Sudan duk da alkawarin tsagaita wuta don babbar Sallah
An yi ta kai hare hare ta sama tare da harba bindigogi masu kakkabe jiragen sama a birnin Khartoum na Sudan duk kuwa da tsagaita wuta da bangarorin da ke rikici da juna suka ayyana don bai wa Musulmi damar gudanar da shagulgulan babbar Sallah.
Wallafawa ranar:
Yakin da ya barke tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun kai daukin gagawa na RSF a watan Afrilu ya yi sanadin babbar matsalar jinkai, kana ya daidaita kusan mutane miliyan 2 da dubu dari 8, inda daga cikin su akalla dubu dari 6 da 50 suka tsallaka zuwa kasashen da ke makwaftaka da Sudan.
Birane 3 da ke gabar kogin Nilu a babbaan birninn kasar da suka hada da arewacin Khartoum da Omdurman sun shafe maakwani 10 cikin yanayi na mummunan rikici tsakanin baangarorin biyu da ke dauke da makamai, a yayin da ya haddasa sake bullar rikicin kabilanci.
Rahotanni sun ce an ci gaba da gwabza fada har a tsakar ranar Laraba a garin Omdurman.
Zalika, kungiyar lauyoyi a yankin Darfur ta ce, dakarun RSF sun kai munanan hare-hare a yankin Manwashi na kudancin Darfur, karo na biyu a cikin kwanaki 5.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu