Isa ga babban shafi

Rikicin Sudan na neman rikidewa zuwa na kabilanci

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matukar fargaba a game da yadda rikicin Sudan ke kokarin rikidewa zuwa na kabilanci a musamman a lardin Darfour, lamarin da ke tilasta wa fararen hula tserewa daga yankin. 

Mutane da dama sun tsare zuwa Chadi sakamakon rikicin Sudan.
Mutane da dama sun tsare zuwa Chadi sakamakon rikicin Sudan. REUTERS - STRINGER
Talla

 

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa sama da mutane dubu 560 ne ke rayuwa a Chadi.

Christophe Garnier, jagoran ayyukan gaggawa a kungiyar agaji ta Medecins Sans Frontieres a garin Adré da ke kasar Chadi, ya bayyana halin da ake ciki yanzu haka inda yake cewa, 

Lalle babban iftila’i ne da ke fuskantar ayyukan jinkai, hakazalika halin da ake ciki na da matukar tada hankali, saboda hatta yadda ake samun kwararar dubban ‘yan gudun hijira zuwa garin Adre, abu ne da ya yi matukar zo wa jama’a a yanayi na ba zata.  Alkaluman da ake samu daga ko’ina, na kara tabbatar da cewa sam babu sauki a lamarin, musamman yanayin da wadannan mutane ke rayuwa anan Adre, gaskiya akwai tausayi. 

  

"Akwai karancin abinci, ba kowa ke samun damar isa ga cibiyoyin kiwon lafiya ba, a zancen da muke yi yanzu haka akwai barazanar barkewar cututuka irinsu kyanda da amai da gudawa a cikin sansanonin ‘yan gudun hijira" inji jami'in. 

  

Ya kuma kara da cewa, akwai dimbin ‘yan gudun hijira da ke rayuwa a filin Allah, ba dakuna, ba tanti, haka su ke rayuwa a fili ba komai, Illa kawai kungiyoyin agaji da suka hada da MSF da kuma Hukumar Kula da ‘Yan gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ke iya kokarinsu domin taimaka wa ‘yan gudun hijira, da kuma tsungunar da su cikin sansanoni. Amma tabbas akwai manyan kalubale a gabanmu a cewarsa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.