Taruwar 'yan tawayen SPLM-N Kordofan ya haifar da fargaba a kudancin Sudan
Bayanai daga wasu mazauna jihar Kordofan da ke Sudan, sun bayyana cewar mayakan ‘yan tawayen kungiyar SPLM-N masu yawan gaske na taruwa, lamarin da ya haifar da fargaba kan yiwuwar barkewar sabon rikici a yankunan kudancin kasar ta Sudan.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Dakarun rundunar ta SPLM-N da aka kiyasta ta kunshi dubun dubatar mayaka dauke da muggan makamai, na karkashin jagorancin babban kwamandansu Abdelaziz al-Hilu.
Har zuwa lokacin wannan wallafa, babu tabbas akan ko wane bangare Hilu zai marawa baya, a rikicin da ya barke tsakanin sojojin gwamnati da dakarun rundunar RSF a birnin Khartoum, ranar 15 ga watan Afrilu.
Rahotanni sun ce a cikin ‘yan watannin da suka gabata an yi artabu tsakanin mayakan ‘yan tawayen na SPLM-N da dakarun musamman na RSF, wadanda a yanzu suka bijirewa gwamnati.
A Khartoum babban birnin kasar ta Sudan kuwa, inda fada ya fi kamari, mazauna yankin sun ce har yanzu ana cigaba da gwabza fada da kuma kai hare-hare ta sama, musamman a ranar Alhamis, duk da sassaucin da aka samu a dalilin yarjejeniyar tsagaita wutar da ta ba da damar kai wa fararen hula agajin gaggawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu