Isa ga babban shafi

ICC da Jamhuriyar Congo za su yi aikin hadin gwiwa na tsaro a tsakiyar Afirka

Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, zasu yi hadin gwiwa wajen tabbatar da tsaro da fatattakar kungiyoyin masu rike da makamai a kasar. 

Yadda wasu mazauna yankin Goima suka fito zanga-zangar adawa da kasancewar dakarun kungiyar gabashin Afirka a kasar.
Yadda wasu mazauna yankin Goima suka fito zanga-zangar adawa da kasancewar dakarun kungiyar gabashin Afirka a kasar. AFP - -
Talla

Babban mai gabatar da kara na kotun Karim Khan ne ya bayyana hakan a wata ziyarar kwanaki hudu da ya kai kasar mai yawan albarkatun karkashin kasa. 

Kungiyoyin masu rike da makamai sun daidaita yankin gabashin kasar, tun daga shekarun 1990 zuwa 2000, tashin hankalin da ya fara fantsama zuwa  kasashen tsakiyar Afirka. 

ICC ta saurari shari'a kan wasu mutane uku da ake zargi da aikata laifukan yaki a kasar ta Congo a shekarar 2002.

Kotun ta kaddamar da binciken ta na farko a Arewa maso gabashin Ituri da ke kasar ta Congo a shekarar 2004.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.