Isa ga babban shafi

Kungiyar JNIM ta saki wani jami'in gwamnatin Mali shekaru 3 bayan garkuwa da shi

Kungiyar ta’addanci ta JNIM da ke biyayya ga Al Qaeda ta saki kantoman karamar hukumar Farako na kasar Mali Ali Cisse Wanda ta yi garkuwa da shi fiye da shekaru 3 da suka gabata.

Wasu mayakan 'yan ta'adda a Mali.
Wasu mayakan 'yan ta'adda a Mali. AFP - HO
Talla

Majiyoyin tsaro da makusantan Ali Cisse sun tabbatarwa RFI batun sako kantoman tun a talatar da ta gabata, wanda tuni ya isa birnin Bamako gabanin mika shi ga ahalinsa a Kolokani da ke cikin yankin Koulikouro, mai tazarar kilo mita 130 daga arewacin Bamako babban birnin kasar.  

Zuwa yanzu dai babu cikakken bayani kan halin da lafiyar kantoman ke ciki, haka kuma babu wata sanarwa daga bangaren mahukumta kan sakin nasa, inda fadar shugaban kasar ta gimtse bakinta ko bayan da RFI ta bukaci karin bayani kan sakin jami’in. 

Ofishin ministan cikin gidan Mali ya bayyana cewa  sakin kantoma Ali Cissé ya zo ne a cikin wani yanayi na musaman domin kuwa a cewar ma’aikatar daga ranar lahadi 28 ga watan mayu kungiyar ta JNIM ta saki akalla mutane 4 da ta jima ta na garkuwa da su.

Mutanen baya-bayan nan da kungiyar ‘yan ta’addan ta saki sun kunshi ‘yan kasar Mali 3 ciki har da tsohon dan majalisar dokoki Abdou Agouzer Maïga, da aka sace a watan da  ya  gabata, sai jami’in kare gandun daji Abdoulaye Kanté, da aka yi garkuwa da shi watanni biyu da suka gabata, kana wani Soja caporal Oumar Diakité, da shima aka sace kusan watanni 3 baya.

Har ila yau kungiyar mayakan ta JNIM ta haska wani faifan videon wani dan kasar Afrika ta Kudu  Gerco Jacobus van Deventer, da ta sace fiye da shekaru 5 da suka gabata. 

Sallamar ta kantoma  Ali Cissé da kuma haska hoton videon da ke nuna shaidar mutanen na raye,  na matsayin tamkar tayin shiga tattaunawa ne tsakanin kungiyar ta JNIM da gwamnatin mulkin sojin ta kasar Mali. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.