Togo na jagorantar taro kan amfani da takin zamani da inganta kasar noma
Gwamnatin kasar Togo ta shirya wani taron kasashen duniya a kan amfani da takin zamani wajen noma da kuma ingantar kasar noman a yankin Afirka ta Yamma.
Wallafawa ranar:
Taron na zuwa ne bayan an dauki dogon lokaci masana aikin noma na gudanar da bincike akan tasirin takin zamani da kuma amfani da shi, kamar yadda aka kaddamar a Jamhuriyar Nijar a shekara ta 2021, wanda ya samar da ci gaban noma a fadin kasar.
Ana saran taron na yau ya sake duba hanyoyin ci gaban fasahar noma da kuma tabbatar da dorewar samar da takin domin inganta gonaki da kuma samar da sabbin dabarun zamani ga manoma.
Taron na rana guda na samun taimakon Bankin Duniya da Cibiyar Bunkasa takin zamani na duniya.
Daga cikin mahalarta taron harda shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu