Isa ga babban shafi

Ghana da Bahamas sun yi alkawarin zurfafa harkokin kasuwanci na hadin gwiwa

Kasashen Ghana da Bahamas sun amince su zurfafa hadin gwiwarsu wajen karfafa harkokin kasuwanci, amma ta hanyar samar da tsarin biza ta bai daya ga duk masu rike da fasfon kasashen biyu.

Tattaunawar wakilan Ghana da Bahamas kenan.
Tattaunawar wakilan Ghana da Bahamas kenan. © ghana/presidency
Talla

Karamin ministan harkokin wajen Ghana Kwaku Ampratwum-Sarpong, yayin ganawa da Firaministan Bahamas, Philip Davis, ya ce shirin zai taimaka wajen karfafa harkokin kasuwancin kasashen biyu.

An kuma yi amfani da tarurrukan don tattauna babban taron zuba jari na Ghana da Bahamas da zza a yi nan gaba.

Firaminista Davis ya ba da tabbacin aniyar kasarsa na sanya hannu kan yarjejeniyar kebance biza tare da yin kira da a gaggauta yin shawarwari tare da kammala wannan yarjejeniya.

Ya kuma jaddada muhimmancin taron zuba jari wajen inganta harkokin tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Mista Ampratwum-Sarpong ya kuma halarci babban taron zuba jari na Ghana da Bahamas wanda aka gudanar a karkashin cibiyar bunkasa zuba jari ta Ghana a ranar 17 ga Mayu, 2023.

Makasudin taron shi ne sake cudanya da al'ummar nahiyar Afirka musamman Bahamas da yankin Karebiya.

Taron dai na da nufin baje kolin tattalin arziki da zuba jari na kasashen biyu domin karfafawa da inganta huldar tattalin arziki tsakanin Ghana da Bahamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.